Tauraruwar Fina-Finan Hausa, Fati Washa kenan a wadannan hotunan inda ta haskaka sosai.
Fati ta saka hotunan a shafinta na sada zumuna wanda suka kayatar da masoyanta.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan yayin da take yawon shakatawa a kasar waje.
Rahama dai ta saka hotunan ne a shafinta na sada zumunta inda aka ganta tana tuka mota, a wasu hotunan kuma aka ganta tana bakin kogi.
Tauraron Fina-finan Hausa kuma mawaki, Sani Musa Danja ya bayyana cewa, Tsohon sarkin Kano da majalisar jihar Kano ta sauke, Aminu Ado Bayero ya hakura ya ajiye lema da sanda ya tafi amma wasu suka zigoshi ya dawo.
Sani Musa Danja ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya saka a shafinsa na sada zumunta inda ya yi tsokaci akan rikicin siyasar Kano.
Yace abin takaici shine duka sarakan ‘yan uwan junane amma an dauko wani abu da zai saka gaba da kiyayya a tsakaninsu.
Sani Musa Danja yayi kiran kawo abinda zai sa zaman lafiya da ci gaba ya dare a Kano.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan inda take tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Rahama ta dora hotonne a shafinta na sada zumunta.