Tauraruwar Fina-finan Hausa, Fati Washa kenan a wannan hotunan nata da suka dauki hankali.
Ta saka hotonne a shafinta na sada zumunta inda tawa masoyanta gaisuwar barka da juma'a.
Tauraron Fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya taya dansa, Ahmad Murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Ali Nuhu ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yawa dan nasa fatan Allah ya masa Albarka.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta saki wadannan hotunan a shafinta na sada zumunta.
Gabon ta kara da cewa, a matsayinta na mace, za'a yi tsammanin tana tsoron tsufa.
Saidai tace sam bata tsoron Tsufa.
Jarumi kuma mawaki Abdul sahir wanda akafi sani da Mallam Ali na kwana casa’in ya ce ya fita daga masana’antar kannywood daga yau alhamis 30-05-2024, yace yayi hakan ne don samar wa kansa nutsuwa.
Idan zaku iya tunawa hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar kano karkashin jagorancin Abba elmustapha ta dakatar dashi daga shiga fina-finan hausa tsawon shekaru 2, sakamakon wani vidiyon da jarumin ya saka, wanda hukumar ke ganin ya sabawa doka da tarbiyyar jihar kano.
Mallam Ali na kwana casa’in ya fice daga kannywood, shin ko waye zai maye gurbinsa acikin kwana casa’in?
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan yayin da take shakatawa a kasar Turkiyya.
Ta saka hotunan a shafinta na sada zumunta inda masoyanta da yawa suka yaba:
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Sarki Aminu Ado Bayero e zabinta.
Ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta i da tace bata hana kowa ya bayyana zabinsa ba.
Sadiya ta saka hoton sarkin tana waka akai.
Rikicin sarautar Kano wadda ya taso bayan da majalisar jihar ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero ta mayar da tsohon Sarki Muhammad Sanusi II akan karagar sarautar ya raba kawunan mutane da yawa a ciki da wajen jihar ta kano.
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN:
Jarumar Finafinan Hausa, Fati Slow Ta Rasú.
Ta rasu ne a wani yankin da ake kira Habasha a kusa da kasar Sudan, inda za a yi jana'izar ta a can, sannan a yi zaman makoki a gidan su dake Unguwa Uku a jihar Kano.
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Tauraruwar Fina-Finan Hausa, Fati Washa kenan a wadannan hotunan inda ta haskaka sosai.
Fati ta saka hotunan a shafinta na sada zumuna wanda suka kayatar da masoyanta.