Friday, January 17
Shadow

Kano

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023 Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP a zaɓén na 2023 da ya gabata, Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya furta hakan a hirarsa da BBC Hausa, ya ce wannan matakin zai inganta harkokin tsaron Najeriya da ya tabarbare a wasu sassan ƙasar. Wane fata zaku yi masa?
Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kano, Siyasa
Hukumar 'yansandan jihar Kano ta bayyana tsaka mai wuya da take ciki kan hukunce-hukuncen kotu har guda biyar da aka yi kan masarautar Kano. Kwamishinan 'yansandan jihar, Mr Usaini Gumel ne ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace sun tattara duka wadannan hukunce-hukuncen 5 sun aikewa da shugaban 'yansanda na kasa yayin da shi kuma ya aikawa da ministan shari'a. Yace suna jiran ministan shari'ar ya gaya musu da wane hukunci zasu yi amfani. Yace da zarar sun samu umarni daga ministan shari'ar, zasu zartas da hukuncin da doka ta amince dashi. Yayi kira kan kafafen yada labarai da su rika tantance labari kamin su yadashi.
‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’

‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’

Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Siyasa
Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya zargi 'yan ƙasar a kan fifita siyasar kuɗi maimaikon zaɓar mutane masu aƙidar da za su iya kawo canji. Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce dimokraɗiyyar Najeriya ta samu koma-baya saboda wasu 'yan siyasa da kan sayi ƙuri'un mutane ta hanyar ba su atamfa ko taliya. A cewarsa, irin wannan tunani na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jefa al'ummar ƙasar cikin halin matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaron da hukumomi suka gaza shawo kansu ya zuwa yanzu. Ya kuma ce rashin iya mulki ne ya haddasa taɓarɓarewar al'amura kamar tsaro da tattalin arziƙi a Najeriya. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana haka a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu ƙusoshin siyasar Nijeriya a wani ɓangare na cika shekara 25 da mulkin dimokraɗiyya karon...

Kowane Musulmi Imaninsa Yana Cika Ne Idan Ya Yarda Tare Da Rungumar Kowace Irin Kaddara Ce Ta Same Shi, Cewar Sarki Sanusi II A Hudubarsa Ta Yau Juma’a

Kano
Daukar ƙaddara mai kyau ko mara kyau yana daga cikin cikar imanin mutum -inji Sarki Sanusi a huɗubarsa ta yau Juma'a Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda zai iya tuhumar Allah dangane da ƙaddara. Sabon sarkin ya faɗi hakan ne yayin huɗubar sallar Juma'a a masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano. Huɗubar dai ta mayar da hankali ne kan imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau. " Duk wanda ya yi imani da Allah shi kaɗai to dole ne ya yi imanin duk abin da Allah ya ƙaddara. Ba a tambayar ubangiji dalilin aiwatar da al'amura. An faɗa mana cewa duk wanda bai yarda da ƙaddara ba cewa daga Allah take, imaninsa bai cika ba. Ya kamata mu zama masu godiya ga Allah a yanayi daɗi ko wuya. Dole ne mu yarda cewa duk abin da ya faru a gare mu ta ƙaddara ce daga Allah,...
Kalli bidiyo:Ana Allah wadai da yanda “Dan Ganduje” ya gaisa da shugaban kasa Tinubu, wasu na cewa bashi da tarbiyya

Kalli bidiyo:Ana Allah wadai da yanda “Dan Ganduje” ya gaisa da shugaban kasa Tinubu, wasu na cewa bashi da tarbiyya

Kano
Wani tsohon bidiyon haduwar Shugaban kasa, Bola Ahmad da shugaban jam'iyyar APC, Dr. Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana a shafukan sada sumunta. A bidiyon, an ga wani matashi wanda aka bayyana da cewa, dan tsohon gwamnan Kanon ne, Ganduje wanda ya gaisa da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Saidai yanayin gaisawar tasu ta jawo cece kuce saboda bai durkusa ba hannu kawai ya bashi suka gaisa. https://www.tiktok.com/@weddings_and_cruise/video/7367361316601728262?_t=8mo5NJgw9kE&_r=1 A al'adar yarbawa dai har kwanciya ana yi wajan gaishe da manya.
Da Duminsa: EFCC ta gayyaci Kwankwaso zata fara bincikenshi kan Naira Biliyan 2.5

Da Duminsa: EFCC ta gayyaci Kwankwaso zata fara bincikenshi kan Naira Biliyan 2.5

Kano
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso dan bincikensa kan zargin almundahanar Naira Biliyan 2.5 na kudin fansho din ma'aikata. Wata majiya daga hukumar tace an gayyaci Kwankwaso kuma ya bayar da bayanai kan lamarin. Saidai an ce za'a ci gaba da bincike. Saidai da aka tuntubi kakakin EFCC ko me zai ce kan lamarin, yaki cewa uffan.
An samu lauyan da zai kare mutumin da ya cinna wa masallaci wuta a Kano

An samu lauyan da zai kare mutumin da ya cinna wa masallaci wuta a Kano

Kano
Babbar kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Kano ta ɗage sauraron ƙarar da take yi kan wani matashi da ya cinna wa masallaci wuta a jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu. A ranar 15 ga watan Mayu ne mutumin da ake zargi a watsa fetur tare da cinna wa masallaci wuta sa'ilin da ake sallar Asuba a ƙaramar hukumar Gezawa ta jiharn Kano. Ya zuwa yanzu lamarin ya haifar da asarar ran mutum 19, yayin da wasu ke ci gaba da samun kulawa a asibiti. A lokacin zaman kotun na yau, alƙali ya bayyana cewa an samu lauyan da zai kare wanda ake zargi, inda ya buƙaci a tattara duk wasu bayanai da hujjoji da suka kamata domin miƙa wa lauyan. Kotun ta ɗage shari'ar ne zuwa ranar huɗu ga watan Yulin 2024. A zaman da kotun ta yi na farko, mutumin ɗan shekara 3...
Aminu Ado Bayero ba zai yi sallar Juma’a a Ƙofar Kudu ba – Ƴansanda

Aminu Ado Bayero ba zai yi sallar Juma’a a Ƙofar Kudu ba – Ƴansanda

Kano
Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta gargaɗi al'umma su guji yaɗa 'labaran ƙarya' da ke cewa sarkin Kano da aka sauke Aminu Ado Bayero zai halarci sallar Juma'a a babban masallacin fadar sarki da ke Ƙofar Kudu. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar ƴansandar ta fitar yau Juma'a, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa. A cewar sanarwar ya kamata al'ummar jihar su yi watsi da labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa sarkin wanda aka sauke zai halarci sallar Juma'ar a Ƙofar Kudu kasancewar ba gaskiya ba ne. Haka nan rundunar ta tabbatar da cewa za ta samar da wadataccen tsaro faɗin jihar. Ana cikin halin ɗar-ɗar a jihar ta Kano tun bayan da Aminu Ado Bayero, wanda gwamnatin jihar ta sauke ya koma birnin na Kano bayan...