Ya ake gane cikin mace
Idan ciki ya kai sati 20, gwajin Ultrasound yakan iya nuna cikin macene ake dauke dashi ko Namiji.
Hakanan akwai gwajin Amniocentesis da shima ake yi wanda ke nuna jinsin jaririn da ake dauke dashi.
Bayannan akwai alamu na gargajiya da ake amfani dasu wajan ganewa ko hasashen cikin mace.
Ciki Yayi sama: Wasu na cewa idan ciki yayi sama sosai, to wannan alamace dake nuna cewa diya macece za'a haifa.
Girman Nono: Hakanan akwai bayanan dake cewa idan nonon mace na hagu yafi na dama girma shima alamace dake nuna mace za'a haifa ba Namiji ba.
Ciwon Safe: Ciwon safe na daya daga cikin dalilan da ake alakanta cikin diya mace dashi inda me ciki zata rika jin kamar zata yi amai, kasala da sauransu.
Kalar Fitsari: Hakanan akwai bayanan dake nuna cewa kalar fitsarin mace ya zama kal...