Maganin zufar fuska
Zufar fuska abune da masu fama dashi ke ci musu tuwo a kwarya.
Yawanci abinda ke kawota shine:
Cin abinci me zafi.
Yanayin Zafi.
Damuwa ko shiga halin matsi.
Razana ko Bacin rai.
Motsa jiki.
Abubuwan da za'a gwada dan magance matsalar zufa a fuska sune:
Yin Wanka akai-akai.
Aje Tawul ko Hankici dan goge zufar.
Amfani da hoda marar kamshi dan tsotse zufar.
A daina cin abinci me yaji ko shan Coffee.
Saka kayan da basu da nauyi wanda iska na ratsasu.
Shan ruwa akai-akai.
Amfani da mafici ko fankar hannu.