Gyaran fuska da aloe vera
Aloe Vera na gyara fatar fuska sosai inda yake kawar da dattin fuska da kara mata haske kuma idan aka duba za'a ganshi a cikin mayukan gyaran fuska da yawa.
Ga jawabin amfanin da Aloe Vera ke yiwa fata da kuma yanda za'a sarrafashi a samu abinda ake so.
Aloe Vera yana maganin duhun fata.
Yana magamin canjawar fuska da zafin rana ke kawowa.
Yana kawar da fatar data mutu a fuska wadda ke kawo duhun fuska.
Yana maganin ciwo a fuska.
Yana maganin kumburin fuska.
Yana maganin cizon kwaro irinsu sauri kudin cizo da sauransu.
Idan za'a sayi man shafawa dage dauke da Aloe vera a duba a tabbatar ba'a hadashi da giya ba ko sauran sinadarai masu kawowa fata illa.
Babbar hanyar samun amfanin Aloe vera a fuska, shine mutum ya hada kayansa a gida.
Yanda ake hada man Aloe Ve...