Monday, January 13
Shadow

Sha’awa

Maganin rashin sha’awa ga maza

Sha'awa
Rashin sha'awa ga maza, matsalace da maza da yawa kan yi korafi akanta, a wannan rubutun, zamu yi bayani yanda matsalar take da abubuwan dake kawota da kuma maganinta. Abubuwan dake kawo rashin sha'awa ga maza Rashin Kwanciyar Hankali: Masana kiwon lafiya musamman na bangaren jima'i sun bayyana cewa, rashin kwanciyar hankali na daya daga cikin abubuwan dake kawarwa namiji sha'awa, misali a yayin da mutum ke cikin tsananin bashi kuma me kudin na nemanka ruwa a jallo, ko kuma an kori mutum daga aiki kuma bashi da hanyar ciyar da iyalansa, da dai sauransu. Kibar da ta wuce misali: Yawan kiba na daya daga cikin abubuwan da masana kiwon lafiya sukace take rage karfin sha'awa. Musamman idan mutum ya zamana me yawan ciye-ciyene barkatai. Rashin Cin Abinci me kyau: Rashin Cin abinci me...

Maganin rashin sha’awa ga mace

Sha'awa
Rashin sha'awa ko raguwar karfin sha'awa ga mata abune dake faruwa yau da gobe kuma yana faruwa da kowace mace a iya tsawon rayuwarta. A wani lokacin zaki ji karfin sha'awarki ya ragu na dan lokaci ko na kwanaki kadan, a wani lokacin kuma zai iya daukar kwanaki da yawa ko ma watanni. Kowane mutum da irin karfin sha'awarsa, wani zai ji yana son yin jima'i kullun wani sai bayan satuka ko bayan watanni kai wata ma a shekara ba zata so yin jima'i sosai ba, kowa da kalar karfin sha'awarshi. Yanayin karfin sha'awarki ba zai taba iya zama a matsayi guda ba a kowane lokaci, ma'ana zai rika yin sama yana kasa, kuma hakan ba matsala bane. Saidai idan rashin sha'awarki yayi yawa kuma ya fara damunki, to ya kamata a tuntubi likita ko a nemi magani. Sannan kuma a sani, mafi yawanci ana g...

Kaikayin Azzakari

Kiwon Lafiya, Sha'awa
Kaikayin Azzakari na daya daga cikin matsalolin da maza kan yi fama dasu, a wannan bayanin, zamu fadi abubuwan dake kawoshi da kuma maganinshi. Abubuwan dake kawo kaikayin Azzakari sune: Infection: Idan ya zamana kana fama da infection akan azzakarinka ko a cikinsa, zaka rika iya yin fama da kaikayin Azzakari. Ciwon fata ko bushewar fata: Idan ya zamana kana fama da yawan bushewar ko wata cuta a jikin fatarka, zaka iya yin fama da kaikayin Azzakari. Cutukan da ake dauka a wajan jima'i: Idan ya zamana ka kamu da daya daga cikin cutukan da ake dauka a wajan jima'i zaka iya yin fama da kaikayin Azzakari. Sabulu da Ake amfani dashi: Kalar sabulun da ake amfani dashi wajan wanka zai iya kawo kaikayin Azzakari. Aske Gashin Gaba: Aske gashin gaba na daya daga cikin abubuwan dake...

Alamomin mutuwar azzakari

Ilimi, Jima'i, Sha'awa
Za'a iya game cewa Azzakari ya mutu idan ya zamana cewa baya iya mikewa da kyau ta yanda mutum zai iya yin jima'i ya gamsu. Hakanan idan ya zamana mutum baya jin sha'awa, ko kuma karfin sha'awarsa ta ragu sosai, shima za'a iya cewa Azzakarinsa ya mutu. Amma idan ya zamana cewa yau mazakutarka ta mike gobe ta ki mikewa, wannan ba matsalar mutuwar azzakari bane, idan ya zamana bata mikewa da kyau ne ta yanda zaka gamsu ko kuma baka dadewa Sam kake kawowa to ya kamata a nemi likita. Abubuwan dake kawo mutuwar Azzakari sun hadada: Yawan kiba. Ciwon Sugar ko Diabetes. Ciwon zuciya. Yawan kitse a jiki. Rashin kwanciyar hankali. Damuwa. Rashin Samun isashshen bacci. Shan giya. Shan taba da sauransu. Ana magance matsalar mutuwar Azzakarine ta hanyoyin: Mo...

Wacece mace mai kyau

Auratayya, Budurci, Gaban mace, Jima'i, Kwalliya, Sha'awa, Soyayya
Shi kyau kala biyune Dana zahiri Dana badini. Kyan Zahiri shine Wanda ake gani da ido, watau fuska me kyau, dogon hanci, fari, da sauransu. Mace me Kyan zahiri za'a iya ganinta fara, doguwa, me matsakaitan mazaunai da matsakaitan nonuwa me fararen idanu, da fararen hakora sannan ta iya wanka. Saidai shi Kyan zahiri yana dusashewa musamman Idan girma ya fara kama mace, shiyasa ake son mace ta hada kyau biyu watau na zahiri dana badini. A lokuta da dama, mace zata iya samun kyan badini amma bata dana zahiri, to idan so samune, mace ta hada duka biyun, amma idan ya zama mutum zaba zai yi tsakanin mace me kyan badini bata dana zahiri da kuma me kyan zahiri bata dana badini, to a shawarce mutum ya dauki mace me kyan badini bata dana zahiri yafi. Shi kuma kyan badini, yawanci ba'a...

Wacece mace mai addini

Gaban mace, Ilimi, Jima'i, Sha'awa, Soyayya
Mace mai addini itace kamila wadda ke da kamun kai, da ilimi na addini dana boko, wadda kuma ta samu tarbiyya irin ta addinin musulunci. Mace mai addini itace wadda bata shigar banza dake nuna tsiraicinta, gashinta a rufe, ba ta sa matsatstsun kaya, bata sa kaya shara-shara Wanda ke nuna cikin jikinta, ta na son saka hijabi. Mace mai addini idan tana da saurayi bata zama kusa dashi su manne suna jin dumin jikin juna. Kuma duk son da take masa bata yadda ya taba jikinta. Mace mai addini tana kokarin kiyaye dokokin Allah da kuma tunatar da Wanda suke kusa da ita suma su kiyaye dokokin Allah. Mace me addini ta iya kalamai na hankali Wanda babu wauta, cin fuska, ko wulakanci a ciki.

Ya ake gane mace ‘yar iska

Sha'awa
Ana gane mace 'yar iska ce ta hanyoyin dabi'u da shigar jikinta ko kalamai da kuma irin mutanen da take ma'amala dasu. Mace wadda take 'yar iska, ko ace ''yar bariki, takan kasance Mara kunya ta yanda zata iya fadar komai ko yin komai ba tare da Shakkar kowa ba. Mace ''yar iska zaka ji kalamanta bata tsaftace su, takan iya fadar kalaman batsa ko na zagi ko cin mutunci ga kowa. Hakanan takan kasance idan tana magana da namiji zata iya kallon sa ido cikin ido ba tare da shakka ba. Hakanan mace ''yar iska, bata damu ba Dan namiji ya taba jikinta ba, ba zata taba yin korafi ba Dan namiji ya taba jikinta ba, asali ma zata iya yin gaisuwa, runguma, ko sumbatar namiji a bainar jama'a ba tare da damuwa ba. Hakanan mace ''yar iska zaka ga abokanta ko kawayenta 'yan iska ne, da wuya t...

Maganin karin sha’awa ga mata

Auratayya, Jima'i, Sha'awa
Idan kina son karin Sha'awa ga wasu shawarwari da masana ilimin kimiyyar lafiyar jima'i suka bada shawarar ayi. Motsa Jiki: Motsa jiki na da matukar muhimmanci ga maza da mata dake son sha'awarsu ta karu. Ba sai an yi gudu ko motsa jiki me wahala ba,ko da kuwa tafiyace ta Akalla mintuna 30 zuwa wata 1 ta isa duk rana. Amma ana son a rika tafiyar da sauri-sauri. A rage shiga damuwa: Yawan saka kai a damuwa yana matukar kashe kaifin sha'awa. Duk abinda zai saka mutum a damuwa ya guje masa. A rika samun isashshen Bacci: Samun Isashshen Bacci na da matukar tasiri wajan kara sha'awa. Mace ta tabbatar tana samun baccin akalla awa 6 zuwa 7. Idan an zo jima'i kada kawai a fara, a rika wasa da juna sosai ta yanda musamman gaban mace zai kawo ruwa dan a ji dadin jima'in. A rika yin ci...

Maganin yawan sha awa

Sha'awa
Sha'awa halittace a jikin kowane dan Adam, kuma kamar yanda kuke ganin wani dogo wani gajere, haka itama sha'awa karfi-karfi ce, ta wani tafi ta wani. Kuma maganar gaskiya babu wani maganin yawan sha'awa na likita da za'a baka a ace kasha. Saidai mazon Allah (SAW) ya baiwa matasa da basu da halin yin aure shawarar su riki yin azumi saboda yana dakushe sha'awa. Amma muddin mutum lafiyarsa qalau kuma zai ci ya koshi kuma yana cikin kwanciyar hankali dolene ya ji sha'awa. Ita sha'awa wata jarabawa itama daga Allah ga dan Adam domin a ga kokarinsa wajan amfani da ita ta hanyar da ya dace, kamar dai yanda dukiya da talauci suke jarabawa ga dan Adam. Kaine da kanka zakawa sha'awarka linzami kada ta kaika ga halaka ko kuma ka biyata ta banyar da bata dace ba. Hanyoyin da za'a bi...

Yadda mace zata gane tanada ni ima

Jima'i, Sha'awa
Mace zata gane tana da ni'ima ta hanyoyi da yawa kamar yanda zamu zayyana a kasa: Idan kina da mazaunai madaidaita: Mace me mazaunai madaidaita watau ba masu girma sosai ba kuma ba kanana ba ana sakata cikin masu ni'ima. Idan kina da Nononuwa madaidaita: Macen dake da madaidaitan Nonuwa itama ana sakata cikin mata masu ni'ima. Mace me shekin Fuska: Macen da ke da shekin fuska na daga cikin wadanda ake sakawa cikin masu ni'ima. Mace me kakkauran lebe: Mace me kakkauran lebe musamman wadda ta iya kula dashi tana shafa masa jan baki ko lipstick yana sheki a ko da yaushe na daya daga cikin wadda ake bayyanawa da me ni'ima. Mace me Madaidaiciyar dundunniya: Macen dake da madaidaitan dunduniya na daya daga cikin wadanda ake bayyanawa a matsayin me ni'ima. Mace me gashi: Macen d...