Daga Yanzu Sarkin Musulmi Ba Shi Da Ikon Yi Wa Kowa Nadi, Cewar Gwamnatin Sokoto
Hakan dai ya biyo bayan wata sabuwar doka da majalisar dokokin jihar ta samar.
Me za ku ce?
ANA BIKIN SALLAH YAN BINDIGA SUN TAFKA MUMMUNAN BARNA A SOKOTO.
Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi
Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito
An ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba.
Allah ta'ala yakawo mana zaman lafiya alfarmar Al-qur'ani.
Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da bai wa ma'aikatan jihar naira 30,000 a matsayin goron sallah.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan muhalli na jihar, Nura Shehu ya aike wa BBC, ta gwamnan jihar ya amince da bai wa duka ma'aikatan jihar da ƙananan hukumomi da masu fansho goron sallar.
Sanarwar ta ƙara da cewa su ma ma'aikatan wucin gadi masu karbar alawus-alawus za su amfana da goron sallar.
''Rukuni na farko ya haɗa da ma'aikatan Jiha, da na ƙananan hukumomi za su karɓi naira 30,000 a matsayin goron Sallah'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce ''rukuni na biyu da ya ƙunshi masu karɓar fansho da masu karɓar alawus-alawus a ƙananan hukumomi da kuma masu karɓar alawus-alawus a hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko waɗanda za su karɓi naira 20, 000 a matsa...
Allah Ya kubutar da Khadija da Hajara da 'yan bìñďìģà suka dauke su a hanyar su ta komawa makaranta a Sokoto, inda yanzu haka suna hannun sojoji kafin su komo gida yau.
Allah Ya kara tsarewa, Ya Kubutar da duk wanda ke hannusu. Muna godiya da addu'a da kuka ta yi.
Daga Muhammad Dahiru Shugaba
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya albashin watan Yuni ga ma'aikatan jihar daga ranar Litinin.
Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar damar yin bikin babbar sallah cikin walwala.
Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce dukkan ma'aikatan jihar, da na ƙananan hukumomi da kuma ƴan fansho ne za su amfana da wannan karamci.
Abubakar Bawa, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da biyan albashin ma'aikata a kan lokaci, kamar yadda ya ce ya zama al'adar gwamantin, biyan albashi a ranar 20 zuwa 21 na kowanne wata, tun bayan karɓar ragamar mulki.
Dama dai gwamnonin jihohin Arewa sun saba yin irin wannan karamci idan aka samu yanayi na gudanar da shagulgulan sallah amma wata bai ƙare ba.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Ali na fuskantar caccaka daga bakunan da yawa daga cikin 'yan Najeriya bayan sakawa wani titi a jihar Sokoto sunan dan shugaban kasa, Seyi Tinubu.
Kafar Peoplesgazette ta bayyana cewa tsohon sunan titin shine Pepsi Road.
Tace kuma a ranar 3 ga watan Yuni ne ya kamata a kaddamar da titin amma hakan bata samu ba.
Gwamna Bala na Jihar Bauchi Ya Halarci Jana'izar Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Allah Ya Karɓi Rayuwarsa A Daren Jiya
Gwamna Bala Mohammed ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Alh Ahmad Aliyu Jalam Kwamishinan ƙananan Hukumomi na jihar Bauchi wanda ya Rasu a sakamakon hatsarin Mota Daga Bauchi Zuwa Jalam
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana shi a matsayin abokin aiki mai himma da kwazo da bayar da gudunmawar ci gaban Gwamnatin PDP a Jihar Bauchi.
Ya ƙara da cewa Rasuwar Ahmed Aliyu Jalam ta haifar da zullumi tare da yin zaman makoki, yana mai rokon Allah ya ba shi AlJannati Firdausi, ya kuma baiwa iyalansa kwarin guiwar jure wannan babban rashi.
Sai dai ya jajantawa ‘yan uwa da al’ummar Jalam a madadin Gwamnatin jihar da jam’iyyar PDP da daukacin al’ummar jihar Bauchi.
Manyan ja...
ALLAH SARKI: Ga Damina Ta Zo Amma Kauyyka Da Dama A Jihar Sokoto Sun Zama Kufai Babu Halin Noma Saboda Matsalar Tsaro
Tun daga1-Tashar Bagaruwa,2-Gidan Auta,3-Teke mai kasuwa,4-Tashar Ango,5- Teke mai Fuloti,6- Gidan Alewa,7- Kuka Majema,8- Kuka Tudu,9-Kuka,10-Inwala,11-Gidan Ayya,12- Santar Dan Hillo,13- Hawan Diram,14- Dakwaro, duk sun watse ba mutane, gashi ruwan shuka sun sauka amma an kori jama'a daga gidajen su maimakon suyi shukar da za su noma, wannan tashin hankalin dame ya yi kama?
Muna kira ga hukumomin da wannan al'amarin ya shafa da suyi gaugawar ɗaukar matakan da suka dace.
Ya Allah albarkacin wannan ranar ta Juma'a ka kawo mana karshen wannan tashin hankalin.
Daga Rabiu Abdullahi KG31/5/202423/11/1445