Wednesday, January 15
Shadow

Ciwon mara bayan saduwa

Ciwon Mara bayan saduwa ko ace ciwon Mara bayan jima’i Abu ne da mata da yawa kan yi korafi akai.

Saidai jin ciwon Mara bayan jima’i a wasu lokutan Matsala ne a wasu lokutan kuma ba matsala bane.

Misali, mace zata iya jin ciwon Mara bayan saduwa idan ya zamana namijin da ta yi jima’i dashi yana da babbar mazakuta kuma a yayin da yake jima’i da ita ya rika tura mata mazakutar cikin farjinta sosai.

Dan kaucewa wannan matsalar, sai mace ta daina yin goho yayin jima’i kuma ta daina kwanciya namiji ya hau kanta, wadannan kalar kwanciyar su ne kesa mazakutar namiji ta rika shiga cikin farjinki sosai Wanda bayan an gama jima’i, zaki iya jin ciwon mara.

Karanta Wannan  Amfanin tsotsar farjin mace

Maimakon goho da kwanciya, mace sai ta kwanta a gefen hagunta ko damarta shi kuma namiji ya kwanta ta bayanta su yi jima’in a haka, ko kuma namiji ya kwanta ta hau kansa, duka wadannan kalar kwanciyar basu bari mazakutar namiji ta Shiga cikin farjinki sosai ta yanda zata rika saki ciwon Mara bayan jima’i.

Hakanan mace zata iya jin ciwon Mara bayan jima’i idan ya zama kalar kwanciyar da ta yi yayin da ake jima’i da ita bata saki jikinta ba, watau ta takure a waje daya.

Mace zata iya jin ciwon mara idan namiji ya zuba mata ruwan maniyyi, wannan na faruwane saboda jikinki yana sarrafa wani Sabon Abu da ya shiga cikinsa, Dan haka ana iya amfani da kwaroron roba ko kuma namiji ya zubar da maniyyinsa a kasa.

Karanta Wannan  Menene maganin wasa da gaba

Hakanan ciwukan da ake dauka a wajan jima’i irin su ciwon sanyi da sauransu suma na iya sawa mace ta ji ciwon Mara bayan jima’i.

Hakanan idan ya zamana mace bata kawo ruwa sosai ta yanda za’a ji dadin yin jima’i daita, watau farjinta a bushe yake, shima hakan zai iya sawa ta ji ciwon Mara bayan jima’i.

Dan magance wannan Matsala, mace na iya amfani da mai irin su man kwa-kwa, ko man zaitun a gabanta Dan yayi santsi da dadin yin jima’i.

Hakanan ana iya zuwa kyamis a saying magungunan ibuprofen, ko naproxen sodium, ko acetaminophen, duka suna maganin ciwon Mara bayan jima’i.

Karanta Wannan  Ciwon mara na sha'awa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *