Friday, May 30
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Saudiyya domin fara zagayen kwanaki hudu a yankin Gulf

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Saudiyya domin fara zagayen kwanaki hudu a yankin Gulf.

Duk yankin da shugaban Amurka ya zaɓa a matsayin wurin da zai fara kai ziyara na nufin yankin na da matuƙar muhimmanci inda ake yi wa ziyarar kallon wani ɓangare.

A watan Mayun 2027, Donald Trump ya sauya abin da aka saba a al’adance inda shugabannin Amurka kan fara ziyara da wurare kamar Canada da Mexico da kuma Turai.

To sai dai kuma maimakon hakan, sai ya fara da ƙasar Saudiyya mai tarin albarkatun manfetur, a zangon mulkinsa na farko, kuma yanzu bayan ya yi kome sai ya zaɓi fara ziyarar da yankin na Gulf daga ranar Talata 13 zuwa Juma’a 16 ga watan Mayu.

Zuwa ƙasashen Saudiyya da Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, ka iya zama ziyarar Trump ta farko a zangon mulkinsa na farko duk da dai cewa ya kai wata ziyarar bazata zuwa birnin Rome a watan da ya gabata domin halartar jana’izar fafaroma Francis.

Kasuwanci

Da yake sanar da tsarinsa na farko a watan Maris, Trump ya bayyana cewa ƙulla alaƙar kasuwanci da ƙasashen Larabawa na cikin manyan tsare-tsarensa, inda ya ce ya cimma hakan ne bayan an yi amsa alƙawarin za a ba shi ɗaruruwan dubban daloli a wata yarjejeniyar kasuwanci da aka ƙulla da kamfanonin Amurka da za su samar da kayayyaki ga Saudiyya da wasu wurare a Gabas ta tsakiya.

“Saboda irin asusun ko-ta-kwana da asusunsu na ƙasashen waje da kuma arziƙin da suke da shi, ƙasashen yankin Gulf na taka muhimmiyar rawa a tattalin arziƙin duniya,” in farfesa Abdullahi Baabood, ɗan ƙasar Oman mai bincike kan al’amuran yankin Gulf.

Bisa la’akari da ƙalubalen tattalin arziƙin da Amurka ke fama da shi a cikin gida, Trump ya fahimci irin alfanun da ke tattare da ƙulla alaƙa da ƙasashen na yankin Gulf masu arziƙi.

a 2017, Trump ya bugi ƙirjin ƙulla alaƙar da ta kai ta tsabar kuɗi har dala biliyan 450 da ta haɗa da ta sayar da makamai da kuɗinta ya kai dala biliyan 110.

Karanta Wannan  Matashin mawakin Najeriya me shekaru 20, Destiny Boy ya sanar da haihuwar dansa na farko

Yanzu kuma ya yi alƙawarin cimma zuba jari da ka iya kai na dala tiriliyan ɗaya tare da Saudiyya.

Bugu da ƙari, Fadar White House ta ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta shiga yarjejeniyar zuba jari da Amurkar mai yawan dala tiriliyan 1.4 a tsawon shekaru 10.

Donald Trump yana fatan nuna “riba” daga tafiyar, in ji Hassan Mneimneh, wani ƙwararre kan yankin Gabas ta tsakiya da harkokin Amurka da ke zaune a Washington, ya shaida wa BBC.

Rashin tabbas na Gabas ta tsakiya

Tsarinn yadda Gaza za ta kasance bayan yaƙi da kuma tunanin Amurka kan ƙasar Iran duka na cikin manyan batutuwan da ke kankane tsare-tsaren Amurkar na ƙasashen waje, da kuma ƙawayen AMurkar da ke yankin na Gulf ka iya amfanar ɓangarorin biyu.

A kwanakinsa na farko-farko a zangonsa na biyu, Donald Trump ya bai wa duniya mamaki inda ya ce ƙasarsa na son ƙwace iko da Gaza domin mayar da birnin zuwa “wurin shaƙatawa”.

Shirin nasa ya ƙunshi mayar da yankin mai mutum miliyan 2.1 da ya ce ƙasashe masu maƙwabtaka ka iya ɗaukar ɗawainiyar yin hakan.

A rangadin nasa, akwai yiwuwar Trump zai nemi kuɗi daga ƙasashen yankin kan sake gina Gaza, in ji farfesa Baabood, duk da cewa akwai yiwuwar zai fi mayar da hankali kan wasu batutuwa na kusa.

“A yanzu haka dai ana sa ran Trump zai nemi ƙasashen na yankin Gulf su taimaka wajen ganin an kammala sakin dukkannin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza,” In ji farfesa Baabood.

A baya-bayan nan ne Amurka ta ƙara yawan dakarunta a yankin Gabas ta tsakiya a daidai lokacin da ta kai hare-haren bam kan ƴan tawayen Houthi a Yemen a ƙoƙarinta na hana su kai hare-hare kan jiragen ruwa a ruwan maliya.

Karanta Wannan  DA DUMI-DUMI: Sheikh Isa Ali Pantami da Sheikh Bello Yabo an hadu ido da ido a Sokoto

Mako guda kuma kafin rangadin na Trump, ƙasar Oman ta shiga tsakanin Amurka da ƴan Houthi.

Mneimneh ya kuma yi amannar cewa akwai yiwuwar Saudiyya ta ƙarfafa wa Amurka gwiwa wajen ganin ta dakatar da hare-harenta kafin ziyarar ta Trump.

A wani hannun kuma, Trump ya kuma yi barazanar kai wa Iran harin bam idan har ba ta dakatar da shirinta na samar da makamin nukiliya ba.

Akwai hanyoyi guda biyu da za a iya shawo kan Iran – ƙarfin soji ko kuma cimma yarjejeniya, Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News a watan Maris, inda ya kara da cewa zai fi son “cimma yarjejeniya.”

Ma’aikatar ƙasashen waje ta Amurka, a wata sanarwa ranar 30 ga watan Afrilu ta ce “gwamnatin Iran na ci gaba iza wutar rikicin Gabas ta tsakiya, na ci gaba da haɓaka shirinta na nukiliya da kuma tallafa wa ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya.”

To sai dai kuma dukkan ɓangarorin biyu na son kauce wa yaƙi, inda kuma ƙasar Oman ke shiga tsakanin Iran da Amurkar dangane da shirin Iran na nukiliya.

Tasirin yankin Gulf a rikicin duniya

Saudiyya ta zama babbar mai shiga tsakanin Amurka da Rasha da Ukraine.

A watan fabrairu ne wata tawagar masu tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha a birnin Riyadh ta tattauna kan yadda za a shawo kan yaƙin da Rasha ke yi da Ukraine.

Taron ya kasance na farko tun bayan fara yaƙin da Rasha ta yi da Ukraine a 2022 wani abu da ya bayyana ƙarshen haɗin kan ƙasashen yamma na ware Rasha.

A watan Maris, Saudiyya ta karɓi ɓakuncin tawagogi daga dukkannin ƙasashen guda uku dangane da tattaunawarsu wajen warware rikicin Rasha da Ukraine.

Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi ƙoƙarin shiga tsakani dangane da sakin fursunonin Rasha da na Ukraine.

Karanta Wannan  Ashe shima Godswill Akpabio ya taba sukar Bukola Saraki bayan da ya canja mai kujerar zama kamar yanda a yanzu fadanshi da Sanata Natasha Akpoti ya samo Asali ne daga canja mata kujera

China da sauran abokan hamayyar Amurka sun fahimci irin muhimmancin da yankin Gulf saboda haka Amurkar ke nuna zaƙuwa wajen ganin ta ƙulla alaƙa da ƙasashen, in ji Farfesa Baabood.

Yiwuwar daidaita tsakanin Saudiyya da Isra’ila

A zangon mulkinsa na farko, Trump ya cimma gagaruwar nasara ta hanyar shiga tsakani wajen ƙulla alaƙar da ke tsakanin Saudiyya da Isra’ila da sauran ƙasashe huɗu na Larabawa da suka haɗa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain da Morocco da Sudan.

Yaƙin basasa a Sudan ka iya daƙile shirin amma kuma sauran ƙasashen guda uku sun bi Misra da Jordan a matsayin ƙasashen Larabawan da suka ƙulla alaƙa da Isra’ila.

Saudiyya wadda ita ce babba a yankin Larabawa da ƙasashen Musulmi har yanzu ba ta fito a hukumance ta amince da Isra’ilar ba.

Wani babban jami’in Saudiyya ya shaida wa BBC a bara cewa “yarjejeniyar na dab” da a cimma ta kafin harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Okotban 2023.

To amma Trump a baya-bayan nan ya nuna cewa ba lallai ne Saudiyya ta buƙaci kafa ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta a matsayin sharaɗi kafin ƙulla ƙawance da Isra’ila.

Saudiyyar dai ta jaddada cewa ba za ta ƙulla alaƙa da Isra’ila ba ba tare da ɗaya ba.

Masu fashin baƙi sun amannar cewa ƙulla ƙawance da Isra’ila na ci gaba da zama wani al’amari mai sarƙaƙiya a tsakanin ƴan Saudiyya.

Yayin da yaƙi ke ci gaba a Gaza, Saudiyya ba ta shirya tattauna wannan batun ba a yayin wannan ziyara, in ji farfesa Baabood.

Ana sa ran Trump zai ci gaba da ƙoƙarin ganin an daidata alaƙar Isra’ila da sauran ƙasashen yankin Gulf, kuma kamar yadda ya ƙara cewa amma duk wani ƙawance a nan gaba tsakanin Isra’ila da Saudiyya ka iya nuni da cimma wata babbar nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *