
Matashiya, Ameera Hashwi me shekaru 25 ta zama Sarauniyar kyau ta garin Wayne County, Michigan kasar Amurka.
Ta kafa tarihi inda ta zama ta farko, Musulma kuma me sanye da hijabi da ta kafa wannan Tarihi.
Ta kammala karatu daga jami’ar Dearborn Heights inda ta karanci Lauya.
Saidai hakan ya tayarwa Amurkawa fararen fata hankali sosai inda suke tambayar ya akai aka bari haka ya faru?