
Rahotanni da hutudole ke sami na cewa yanzu haka tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya shiga hannun EFCC.
Tun ranar Juma’a ne dai EFCC ta yi nasarar cafkeshi inda aka fara masa tambayoyi shi da wasu tsaffin ma’aikatan da aka kamasu tare.
Rahotannin sun ce zai kwashe karshen makonnan a hannun EFCC inda za’a ci gaba da tuhumarsa.