
Rahotanni daga jihar Naija na cewa, an kama General, Mohammed Ibrahim Gana, me ritaya wanda kuma shine Danmagayakin Nupe bisa zargin cewa, yana cikin wadanda suka yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki.
An kamashi ne bayan an kama dansa wanda yanzu haka soja ne me suna Lieutenant Colonel Sadiq Ibrahim-Gana.
Sahara Reporters ce ta ruwaito lamarin inda tace Gana na cikin sojoji 34 da ake tsare dasu bisa zargin wannan shiri.