
Dan majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun bayyana wanda suke so a baiwa Mataimakin Gwamnan jihar Kano.
Duka su biyun sun bayyana Murtala Garo a matsayin wanda suke son a baiwa mataimakin Gwamnan jihar ta Kano.
Doguwa ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Rahoton yace an cimma matsayar a zabi garo a matsayin mataimakin Gwamnan jihar Kano ne bayan wani zama da masu fada aji na jam’iyyar APC a jihar Kano suka yi ranar Asabar.
Kuma kaso 90 cikin 100 na mutanen suka ce sun amince a zabi Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar.