Friday, January 16
Shadow

Da Duminsa: Gwamnati ta fitar da gargadin Ambaliyar ruwan da za’a kwashe kwanaki 5 ana yi a jihohi 19, karanta jadawalin Jihohin

Gwamnati tacw za’a kwashe kwanaki 5 ana ruwan sama a jere wanda hakan zai iya jawo ambaliyar ruwa a jihohi 19 da furare 76.

Bangaren kula da ambaliyar ruwa na ma’aikatar Muhalli ne ya fitar da wannan sanarwar.

Hakan na zuwane yayin da ambaliyar ruwan tuni ta shiga jihohin Gombe, Plateau, Ogun, Anambra, Delta, da Legas a ranar Talata.

Wannan ambaliyar ruwa a cewar sanarwar zata fara ne daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Augusta.

Garuruwan da lamarin zai shafa sun hada da Akwa-Ibom (Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang); Bauchi (Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a); Ebonyi (Abakaliki, Echara, Ezilo); Cross-River (Ogoja Edor, Obubra); Nasarawa (Keana, Keffi, Wamba); Benue (Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya); Kaduna (Jaji, Kafancha, Birnin-Gwari, Zaria) da Katsina (Bindawa, Bakori, Daura, Funtua).

Karanta Wannan  Ba'a isa a hanamu yin hukunci da shari'ar musukunci ba>>Musulman Yarbawa suka mayarwa da Gwamnoninsu Martani

Sauran sune Kebbi (Bagudo, Birnin-Kebbi, Bunza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa, Shanga, Ribah, Sakaba, Saminaka, Yelwa, Gauri-Banza); Kano (Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Kano, Karaye, Tundun-wada, Wudil, Kunchi); Niger (Kontagora, Rijau, Ringim); Plateau (Mangu); Taraba (Donga, Takum); Jigawa (Diginsa, Gumel, Dutse, Gwaram, Hadejia, Miga); Yobe (Machina, Potiskum); Zamfara (Anka); Sokoto (Sokoto, Wamakko); Borno (Biu); and Gombe (Bajoga).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *