Wednesday, March 18
Shadow

Da Duminsa: Gwamnatin Kano ta bayyana sarkin da ta amince yayi hawan Sallah a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar sarkin data amince yayi hawan Sallah a Kano.

Gwamnatin tace Sarki Muhammad Sanusi II ne ta amince yayi hawan saidai ta saka doka dan gujewa tashin hankali.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba inda yace an saka dokoki wajan hawan ne bayan bayanan sirri da suka samu cewa wasu na shirin tayar da rikici a wajan hawan Sallar.

Da Dumi Dumi

Gwamnatin Kano ta ce Sarki Muhammad Sanusi II ne zai yi Hawan Sallah

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fitar da sabbin tsauraran matakai kan bukukuwan Sallah domin kauce wa rikici da tabbatar da zaman lafiya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo da Duminsa: Wanda ya kirkiri Bidiyon AI na Sultan ya fito ya bayyana kansa inda yace DSS su saki Sultan su kamashi

A cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar ya fitar, gwamnatin ta ce ta samu sahihan bayanan sirri daga Kwamitin Tsaro na Jihar da ke nuna yiwuwar wasu su haddasa rikici yayin bukukuwan Sallah a jihar.

Bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano, gwamnatin ta amince da cewa Hawan Idi zai gudana karkashin jagorancin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, daga Kofar Mata zuwa fadar sarki ta Kofar Fatalwa, yayin da Hawan Nasarawa zai gudana amma ba tare da hawa dawakai ba.

Sai dai gwamnati ta sanar da dakatar da Hawan Daushe, Hawan Fanisau da Hawan Dorayi na wannan Sallah, domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaro.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Na yi mamaki da naji ance Kwankwaso zai dawo APC, saboda a baya ya Zhaghi shugaba Tinubu sannan yace masu shiga APC Mahaukata ne>>Inji Ganduje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *