
Rahotanni sun bayyana cewa, babbar kotun tarayya dake Abuja ta saurari karar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya shigar inda yake kalubalantar tsareshi da ake yi da kuma zarge-zargen da ake masa.
Me magana da yawun Malam Nasiru, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana hakan inda yace a yau, Kotun na sauraren karar take hakkin malam da ya shigar.
Kotu taji duka bangarorin me kara da wanda ake kara inda ta daga karar zuwa ranar 27 ga watan February dan baiwa wanda ake karar damar tattara bayanai.