
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da dokar ta baci da ya kakabawa jihar Rivers ta tsawon watanni 6.
Shugaban ya bayyana dawo da gwamnatin farar hula ta Gwamna Simi Fubara.
Shugaban a sanarwar da ya fitar da yammacin ranar Laraba yace ranar 18 ga watan Satumba Gwamnatin farar hula ta jihar zata ci gaba aiki.