Tuesday, February 3
Shadow

Da Duminsa: ‘Yan Bìndìgà sun tare ‘yansandan Najeriya sun kashe 2 daga ciki

Tawagar ‘yansandan Najeriya da suka fita aiki a karamar hukumar Jos dake jihar Filato sun gamu da kwantan baunar ‘yan Bindiga inda suka afka musu suka kashe ‘yansanda 2.

Lamarin ya farune akan titin Little Rayfield Road da misalin karfe 7:30 pm.

Ana zargin dai ko ‘yan Fashi ko masu garkuwa da mutanene suka afkawa ‘yansandan.

‘yansandan da aka kashe sune Inspector Fatoye Femi da Inspector Dafur Dashit.

An kama daya daga cikin maharan me suna Auwal Ali.

Karanta Wannan  Abin na min Takaici matuka idan aka ce wai in an kama Tsageran dashi a kare hakkinsa na Bil'adama, Kawai ni a nawa ra'ayin a shyekye dan banza dan baiwa amfani>>Inji Sanata Ali Ndume

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *