Tuesday, March 17
Shadow

Da Duminsa:An yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin Mùlkì>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa an yi yunkurin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Jhuyin Mùlkì.

Hakan ya fito ne daga bakin daraktan yada labarai na hukumar ta sojojin Najeriya, AFN Samaila Uba.

Ya bayyana cewa an kamma Bincike kuma an tabbatar da cewa sojojin da ake zargi sun yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki ne.

Yace dan haka an mikawa hukumomin soji da suka dace lamarin dan a dauki matakin da ya dace,.

Sanarwar ta ranar Litinin tace Nan gaba kadan za’a gabatar da sojojin a gaban kotun sojoji dan hukuntasu.

A watan October da ya gabata ne dai aka soke faretin ranar ‘yanci da aka saba yi, wanda kafafen yada labarai suka ce yunkurin Juyin mulki ne yasa aka yi hakan.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Akwai wanda yace mana idan Izala Gaskiya ce kada Allah yasa ya kai shekara me zuwa, kuma baikai labari ba, kamin shekara ta zagayo ya riga mu gidan gaskiya>>Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Saidai chukwu sojojin a wancan lokacin ta musanta hakan.

Amma a sanarwar data fitar yau, Litinin, Hukumar sojojin ta tabbatar da yunkurin Juyin mulkin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *