
Tsohon sanata daga jihar Kebbi Sanata Bala Ibn Na’Allah ya bayyana cewa da yawan ‘yan majalisa bayan sun bar majalisar basa iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansu.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Trust TV.
Yace yawanci ‘yan majalisa idan suka yi ritaya bayan shekara daya zaka ga basa iya biyan kudin makarantar ‘ya’yansu.
Yace wannan yana faruwane musamman ga wadanda dama can basu da wata sana’a sai siyasar.
Yace yawanci mutane suna tsammanin wasu manyan kudi ne ake samu a majalisar Amma a gaskiyar zahiri ba haka bane.