Thursday, January 16
Shadow

Daga cikin Naira Biliyan 13 da aka mana Alkawari na tallafi daga mutane daban-daban, Naira Biliyan 4.5 kadai suka shigo hannunmu>>Inji Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin jihar ta karɓi kusan naira biliyan huɗu da rabi daga cikin fiye da naira biliyan 13 da aka yi musu alƙawari a matsayin tallafi ga waɗanda ibtila’in ambaliya ya shafa a Maiduguri.

“…naira 4,441,494,902.81 ne suka shigo hannunmu daga cikin alƙawuran N13,195,500,000 da aka yi mana. Za mu ci gaba da sanar da jama’a duk lokacin da aka samu ƙarin shigowar kuɗi” In ji gwamna Zulum.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kafa kwamitin mutum 35 da zai kula da raba wannan tallafi ga waɗanda al’amarin ya shafa.

Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijjani ya fitar, ya wallafa a shafin X na gwamna Zulum, gwamnan ya ce kwamitin zai ƙunshi wakilai daga hukumomi da dama da suka haɗa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da takwararta ta ICPC da kuma hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.

Karanta Wannan  Kasar Equatorial Guinea ta hana sauke bidiyo saboda hana yada Bidiyoyin bàtsà na jami'in gwamnati guda 400 da aka ganshi yana làlàtà da matan mutane

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa masu ba wa gwamnan shawara da wakilan hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) da ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da ma’aikatar kuɗi da ta mata da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da sauransu.

Gwamna Zulum ya buƙaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen sauke nauyin da aka ba su da kuma yin gaskiya.

“Za mu tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace, za mu tsaya mu ga tallafin ya kai ga mutanen da aka yi domin su,” in ji Zulum.

Ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da ganin an sake gyara wurare kamar asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji.

Mutane da dama dai, musamman masu hannu da shuni suka bayar da tallafin kuɗaɗe da kuma kayan abinci zuwa ga waɗanda ambaliyar Maiduguri ta shafa.

Ya ce sun samu karɓar tallafi da ya kai naira biliyan 4.4 zuwa cikin asusun tallafin jihar.

Karanta Wannan  Aikin Ofis yayi karanci a kasar China, Matasa masu digiri na biyu dana uku watau Masters da PhD sun koma tuka motocin haya da aiki da gidajen abinci da sauran sana'o'in hannu dan dogaro da kai

Gargaɗin Zulum ga ƴankwamitin rabo

Gwamna Babagana Umara Zulum ya gargaɗi mambobin kwamitin da su yi gaskiya da riƙon amana yayin rabon tallafin.

“Ga mambobin kwamitin nan, ina kira gare ku da ku sauke wannan nauyi bisa gaskiya da adalci. Dole ne mu ɗauki alhakin duk wani nauyi da aka rataya a wuyanmu.” In ji gwamnan Zulum.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin bai wa ƴankwamitin alawus ɗinsu daga aljihun gwamnati ba da kuɗin tallafin ba, inda ya ce za a raba tallafin ne ga waɗanda abin ya shafa ɗri bisa ɗari ba tare da rage ko kwabo ba.

Farfesa Zulum ya ƙara da cewa gwamnati za ta gyara asibitoci da tituna da gadoji da ambaliyar ta lalata.

Amurka ta aike da tallafi zuwa ga Maiduguri

Amurka ta aika tallafin abinci zuwa ga waɗanda ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wata sanawarwa da hukumar raya ƙasashe ta gwamnatin Amurkar wato USAID ta fitar, ta ce za ayi amfani da ƙungiyoyin agaji na MDD da kuma waɗanda take hulɗa da su wajen bayar da tallafin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yansanda sun kama 'yan kasar China 80 suna ayyukan damfarar yanar gizo a Abuja

“Abin damuwa ne matuka ganin yadda ambaliya ta ɗaiɗaita al’ummomi a Maiduguri da wasu sassan jihar Borno, abin da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi. Muna miƙa sakon ta’aziyya zuwa ga iyalan da abin ya shafa,” in ji Amurka.

USAID ɗin ta ce za ta yi aiki da shirin samar da abinci na duniya (WFP) wajen kai tallafin abincin zuwa sansanoni huɗu da aka tsugunar da waɗanda ambaliyar ta ɗaiɗaita, kuma an samu kai ga mutane sama da 67,000 a cikin kwanaki da suka gabata.

Shi ma WFP ya ce yana taimakawa mata masu ciki da kuma yara ƴan ƙasa da shekara biyar wajen samun abinci mai gina jiki.

Haka kuma, Amurkar ta ce tana taimakawa wajen kai abinci wuraren da ke da wahalar kai wa a Maiduguri da kuma faɗin jihar Borno ta hanyar amfani da jiragen sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *