A yayin da al’ummar jihar Sokoto ke fama da matsananciyar matsalar tsaro, mutane a karamar hukumar Sabon Birni sun biya ‘yan Bindiga makudan kudade a matsayin kudin fansa.
Wata kungiya me suna, Gobir Development Association ta bayyana cewa mutanen yankin sun biya Naira Biliyan 160 a matsayin kudin fansa ga ‘yan Bindigar.
Shugaban kungiyar, Idris Alhassan Gatawa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace kuma an tafka asarar Naira Biliyan 2 a hannun ‘yan Bindigar.
Ya kuma bayayyana cewa, mafi yawan gonaki mutane basa iya zuwa saboda ayyukan ‘yan Bindigar wanda hakan ya kawo wahalar tattalin arziki da kuma karancin abinci me gina jiki.
Ya roki gwamnati data kawowa yankin nasu tallafi.