
Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida,IBB ya bayyana dalilin da yasa ya kifar da Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakane a littafinsa da ya wallafa wanda yayi bayani kan yanda ya gudanar da aikinsa.
IBB wanda shine shugaban ma’aikatan Gwamnatin Buhari a wancan lokacin yace bai gamsu da yanda Buhari ke gudanar da mulki ba shiyasa ya masa juyin mulki.
IBB yace tare suke mulki amma sam yaga tsare-tsaren Buhari basa kawo ci gaba a kasar shiyasa ya kifar dashi a shekarar 1985.