Thursday, February 12
Shadow

Darajar naira ta yi faɗuwar da ba a taɓa gani ba a baya-bayan nan

Darajar kuɗin naira a Najeriya ta yi faɗuwar da aka daɗe ba a gani ba a kan dala a wannan makon a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje.

Ana alakanta hakan da ƙarin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba wa ƙasar.

Bayanai kan hada-hadar canji daga babban bankin ƙasar CBN, sun nuna darajar ta faɗi zuwa N1,552.53 a kan duk dala 1 a ranar alhamis, saɓanin N1,531.25 duk dala da aka samu ranar Laraba.

Karanta Wannan  Gaskiya Sheikh Maqari yayi, Haka ya kamata kowane malami ya kasance, Ya kamata ace ana sabunta Addinin Musulunci, yayi daidai da Zamani>>Inji Gfresh bayan da Sheikh Maqari ya fashi fatawar zai iya ci gaba da yin Bidiyo da matarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *