Monday, June 2
Shadow

Dattawan APC sun ce basu son Kwankwaso ya koma jam’iyyar

Raɗe-raɗin dawowar Kwankwaso jam’iyyar APC mai mulki, na cigaba da fitowa fili.

An samu rudani a sakateriyar jam’iyyar APC, a ranar Talata, bayan da Shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Ministan Jiha na Harkokin Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Ata, suka yi sabani kan daowawar Kwankwaso jam’iyyar APC.

Yayin da Minista Ata ke cewa Kwankwaso – wanda kuma tsohon Ministan Tsaro ne – ya rasa karbuwa a Kano kuma siyasar sa na dab da mutuwa, Ganduje ya ce APC ba lallai ta ki karbansa ba, yana mai cewa “aboki a lokacin bukata, aboki ne na gaskiya.”

Ata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Ganduje a sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, ya bayyana cewa matsin lambar siyasar da Kwankwaso ke ciki ne ke sa shi kokarin dawowa APC, yana mai cewa har Kwankwasiyya na dab da rushewa a Kano.

Karanta Wannan  Ban damu sai na koma Kujerar Gwamna ko ta halin kaka ba>>Gwamnan Jihar Rivers Simi Fubara

A cewarsa, sai dai idan Ganduje – wanda ke matsayin jagoran APC a Kano – ya amince da hakan, ba zai yiwu a karbi Kwankwaso, wanda ke jagorantar jam’iyyar NNPP, ba.

Minista Ata ya ce, “Kwankwaso ba shi da tasiri a Kano yanzu. Ba mu gayyace shi zuwa APC ba, shi ne ke kokarin dawowa. Zan tabbatar muku da cewa hatta Shugaban Kasa yana da cikakken bayaninsa daga matakin tushe a Kano. Bai da wani tasiri yanzu, kuma ba wani madadin da yake wakilta. Wannan matsayarmu ce – sai dai idan Shugabanmu (Ganduje) ya amince da karbarsa.”

Ya ci gaba da cewa, “Na kasance dan Majalisar Dokoki tun 1999 lokacin da Kwankwaso ke Gwamna. Na san shi sosai. Bai da tasiri yanzu a Kano. Ba mu da wata yarjejeniya da shi – sai idan Shugaban Kasa ko Shugaban Jam’iyya ya ce a karbe shi.”

Karanta Wannan  Kalli Kayataccen hoton Nafisa Abdullahi

Amma Ganduje ya bayyana cewa ba dace APC ta yi watsi da Kwankwaso ba, duba da cewa mutum ne da aka kaurace wa, kuma bai kamata a bar shi cikin duhu ba.

A cewarsa: “Idan kifin ruwa ya fara fita daga ruwa, shi ne abin da ke faruwa yanzu. Idan ruwa ya fara bushewa, dole kifi ya nemi sabon ruwa. Hakan ke faruwa yanzu. Ba zan ce ba za mu karbe shi ba.”

Ya kara da cewa: “Idan ka ga danka na kokarin gudu zuwa inda zai samu mafaka, kuma kai babba ne a gida mai fadi, to abin da ya dace shine ka karbe shi. Ba za mu ce ba za mu karbe shi ba, domin aboki a lokacin bukata, aboki ne na gaskiya. Mutum da aka kaurace wa, bai kamata mu bar shi cikin duhu ba.”

Karanta Wannan  Hotuna: Dandazon Jama’a Sun Halarci Zaman Fadan Sarki Aminu Ado A Yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *