
A yayin da rahotanni suka tabbatar da cewa mutane da dama sun rigamu gidan gaskiya a hannun Hukumomin Tsaro na NSCDC a jihar Naija.
Daya daga cikin matasa masu hakar ma’adanai wanda ya tsira ya bayar da labarin yanda lamarin ya faru.
Jami’an NSCDC sun kama Matasan da ake zargin da hakar ma’adanai ba bisa ka’idaba inda aka kaisu aka tsare wanda a inda ake tsare dasu ne rai yayi halinsa.
Tuni dai aka dakatar da kwamandan Hukumar NSCDC na yankin inda aka fara gudanar da bincike.