Tuesday, March 18
Shadow

Duk da karar da Sanata Natasha Akpoti ta kai majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Dattijai tace dakatarwar data mata na nan daram ba Fashi

Majalisar dattijai tace dakatar war datawa Sanata Natasha Akpoti na nan Daram ba fashi.

Ta bayyana hakane bayan zaman da manyan majalisar suka yi inda aka so kafa kwamiti dan warware matsalar dake tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti.

Saidai sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa, janye dakatarwar da akawa Sanata Natasha Akpoti zai nuna cewa majalisar na da rauni dan haka kamata yayi jaddada dakatarwar da aka mata.

Hakan kuwa aka yi inda sanata Danjuma Goje da Abdul Ahmed Ningi, da sauransu duk suka amince da wannan matsaya.

Hakan na zuwane bayan da sanata Natasha Akpoti ta kai maganar gaban majalisar Dinkin Duniya.

Karanta Wannan  Alawus din da kuke dauka me yawa da yanda kukafi kowa kudi na baiwa 'yan Najeriya haushi sosai>>Batist Church ta gayawa Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *