Sunday, March 16
Shadow

Duk da yake nasan cewa tsare-tsaren gwamnatina sun jefa ‘yan Najeriya cikin Mawuyacin hali amma kasar ba zata dore ba da an ci gaba da biyan tallafin man fetur>>Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya ba zata dore ba da an ci gaba da biyan tallafin man fetur.

ya bayyana hakane a wajan taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da ya gudana a Fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.

Shugaban ya bayyana cewa, dolene tasa ya cire tallafin man fetur din amma kuma kowace jiha na samun kudi nunki uku fiye da yanda take samu kamin ya hau mulki.

Shugaban ya fadi wannan maganane a yayin da bayan cire tallafin man fetur din mutanen Najeriya da yawa suka shiga cikin halin kaka nikayi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *