Friday, December 5
Shadow

Fadar Shugaban kasa ta aikawa Sowore sako a Asirce cewa ya goge maganar da yayi akan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Mawallafin Jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, fadar shugaban kasa ta aika masa da sakon cewa ya goge kalaman da yayi akan shugaban kasar na cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me laifi ne kuma yayi karyar cewa ta magance cin hanci da rashawa a kasar Brazil.

Sowore yace me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya aika masa da sakon.

Yace Onanuga ya gaya masa cewa bai fahimci abinda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke nufi da maganar da yayi gane, Tinubu yana nufin ya magance matsalar rashawa da cin hanci ne a bangaren hadahadar kudaden kasar waje ba wai Najeriya gaba dayanta ba.

Karanta Wannan  Shin da gaske akwai Baraka tsakanin Buhari da Tinubu? Ji bayani dalla-dalla

Sowore yace Onanuga ya aika masa da wannan sakonne ta WhatsApp.

Saidai Sowore yace duk da haka ba zai goge sakon nashi ba dan wannan yana nufin za’a rika tursasawa mutane akan irin fahimtar da ya kamata suwa shugaban kasa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *