
An wayi garin yau, Litinin da fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na Gwamna Bala Muhammad a titunan Bauchi.
Rahoton yace an kika fastocin a guraren da suka fi faukar hankali irin su shataletale da jikin pol din wutar lantarki da sauransu.
Masu lika fastar sun ce wasu ‘yan siyasa Ya’u Ortega da Talolo ne suka basu aikin lika fastar.
Daily Trust ta yi kokarin jin ta bakin wadanda suka bayar da aikin lika fastar amma abin ya ci Tura.