
Golan kungiyar Kwallon kafa ta Real Zaragoza ya dauki hankula bayan da aka bashi jan kati.
Ya ture dan wasan kungiyar Huesca da suke buga wasa da ita inda aka bashi jan Kati, saidai ya kara zuwa ya mangare wani dan wasan kungiyar.
Lamarin dai ya kawo hatsaniya a filin wasan.
Wasan dai ya tashi Huesca na cin Real Zaragoza 1-0.