Tuesday, May 6
Shadow

Gwamna Abba Gida-gida ya raba fom din JAMB kyauta guda 10,000 ga ɗalibai

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya fara rabon don din JAMB ga ɗaliban makarantar sakandire su dubu 10 a jihar.

A wajen bikin kaddamar da shirin, gwamna Yusuf, wanda Kwamishinan Ilimi, Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya kuma kaddamar da fara bada horo kan zana jarrabawar ta na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Ya kuma ce gwamnan ya yi alkawarin daukar nauyin kai daliban wajen horon kyauta ba tare da sun biya kudin mota ba.

Ya kuma ce duk waɗanda su ka lashe jarrabawar gwamnati za ta zaba musu makaranta mai kyau.

Karanta Wannan  Rikicin Jam'iyyar NNPP: Gwamna Abba Gida-Gida yaki daga waya bayan sa Kwankwaso ya kirashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *