Friday, December 26
Shadow

Gwamnati ta kwace gidan dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya da kudin sata a kasar Amurka

Gwamnatin tarayya ta kwace gidan Dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya a kasar Amurka da kudin sata.

A watan Augusta ne aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samunsa da laifin rashawa da cin hanci.

An sameshi da laifin karbar cin hanci har dala Miliyan $2.1 daga wani kamfanin mai me suna Addax Petroleum da zummar cewa zai samarwa da kamfanin lasisin hakar danyen man fetur a Najeriya.

Kuma ya sayi gidanne a Valencia dake California kasar Amurka.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Saboda munin hare-haren da aka kai jihar Benue, na dakatar da duk wani aiki da nake zan kai ziyara jihar Benue>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *