Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Kano na neman a kama Ganduje, saboda yunkurin kafa kungiyar tsaro ta sa kai

Majalisar zartaswar jihar Kano ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike tare da kama tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa wasu kalamai da ta bayyana a matsayin tsokana da kuma tada zaune tsaye kan matsalar tsaro a jihar.

Hakan ya biyo bayan tattaunawa ne a taron majalisar zartarwa karo na 34 da aka gudanar a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar Kano, inda ƴan majalisar suka yi nazari kan kalaman Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin na baya-bayan nan, inda suka yi zargin cewa Kano na kara fuskantar matsalar ƴan fashi da kuma bayyana shirin ɗaukar mutane 12,000 aikin ƴan sandan rundunar tsaro mai suna Khairul Nas.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Gwamnin Ban tausai inda Hukumomin sojan Najeriya suka kama wani soja me mukamin Kanal saboda yayi korafin an ki kara mai matsayi zuwa Brigadier General

Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske game da sakamakon taron a ranar Juma’a, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce kalaman na iya kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da tsaro da gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi.

Majalisar ta ƙara da cewa, ƙasa da sa’o’i 48 bayan an yi waɗannan kalamai, wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kutsa kai cikin wasu al’ummomin kan iyaka a jihar – lamarin da ta ce “ya sanya ayar tambaya kan ko an furta kalaman tare da wata masaniya ce ko kuma suna da alaƙa da harin.”

Karanta Wannan  INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Jabir Lawan Kenan Da Masù Kwàcen Waya Suķa Kàshè A Kano Bayan Sun Kaŕbè Masa Waýa

“Ba mu san abin da Ganduje ke nufi da waɗannan kalamai ba saboda haka muna kira da a kama shi, dole ne a bincike shi saboda ba za mu iya kallon sa yana kawo mana cikas a zaman lafiya a jihar ba.” in ji shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *