Thursday, June 5
Shadow

Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 670 Don Siyan Motoci Ga Sunusi Lamido Sanusi, Duk Da Kalubalen Da Al’umma Ke Fuskanta

Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 670 Don Siyan Motoci Ga Sunusi Lamido Sanusi, Duk Da Kalubalen Da Al’umma Ke Fuskanta.

A wani lamari da ke kara daukar hankalin jama’a, gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware zunzurutun kudi har Naira ₦670,000,000 don sayen motoci na alfarma ga tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.

Bincike ya nuna cewa kudaden za su fito ne daga asusun jihar Kano da kananan hukumomi 44, inda kowace karamar hukuma za ta bayar da ₦15,227,272 domin cika adadin kudin. Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata takarda mai lamba MLG/SNSNTLGD/166T/6 da aka fitar ranar 25 ga Maris, 2025. Kamfanin da aka ba kwangilar siyan motocin shi ne Sottom.

Karanta Wannan  A kokarin da masana kimiyya ke yi na Gano karshen Kasar da muke takawa, sun samu ci gaba inda suka yi nisa sosai a hakar da suke yi amma har yanzu basu kai karshen kasar ba

Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar Kano ke fuskantar manyan matsaloli na karancin ruwa da wutar lantarki, wanda hakan ke haddasa karancin ayyukan yi da koma bayan tattalin arziki.

Masu lura da al’amura na tambayar ko ya dace gwamnati ta fifita kashe makudan kudade kan kayan alfarma a lokacin da al’umma ke cikin tsananin bukata da halin kunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *