Friday, December 6
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1, karanta yanda zaku nema

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, ta fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1 da aka nema a baya.

Bashin dai ana bayar dashi ne ga mutane wanda kamfanoninsu ko kasuwancinsu ke da rijistar CAC.

Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 75 dan baiwa mamfanoni ko kasuwanci masu rijista bashin Naira Miliyan 1 kowannensu.

Bashin dai baya bukatar ka bayar da jingina saidai akwai kudin ruwa na kaso 9 cikin 100.

Ana bayar da bashinne ta hanyar bankin Bank of Industry.

Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar samar da ayyuka da kananan masana’antu Temitola Adekunle-Johnson ne ya bayyana haka a yau Laraba.

Tuni dai aka fara wannan shiri a jihohin Ogun, Bauchi, Enugu, Kaduna.

Karanta Wannan  Mutane 243,000 sun daina biyan kudin talabijin ta DSTV a Najeriya saboda tsadar rayuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *