Gwamnatin ta sanar da amincewa da fitar da Naira N252.89bn dan ci gaba da gyaran titin Abuja zuwa Kano.
Ministan Ayyuka, Dave Umahi ne ya tabbatar da hakan inda yace za’a gabatar da wannan magana a gaban majalisar zartaswa ta kasa dan amincewa da ita.
Kamfanin da aka baiwa kwangilar wannan aiki shine Infoust Nigeria Limited.
Ministan yace za’a yi amfani da fasahar zamani dan gyaran titin wanda ke saukaka tafiye-tafiye da cinikayya tsakanin kudu da Arewa.