
Gwamnonin arewa da kuma sarakunan gargajiya na gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin.
Taron wanda ke gudana a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, zai kuma tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin.
Gwamnonin jihohin Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da kuma Zamfara na cikin waɗanda ke halartar taron.
A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.