Sojojin Najeriya 196 ne suka ajiye aiki saboda rashin gwarin gwiwar yin yaki da kuma cin hanci da rashin lafiya.
Sojojin sun bukaci ajiye aikin ne bisa radin kansu inda suka mika bukatarsu ga shugaban sojojin Najeriya, Lt Gen Taoreed Lagbaja.
Hakanan Shugaban sojojin ya bayyana amincewarsa akan ajiye aikin nasu.
Majiyar Sahara Reporters tace sojojin duka masu kananan mukamai ne kuma sun bayyana ra’ayin shiga aikin soja a kasashen Amurka da Turai.