
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan daba sun farwa kasuwar wayoyi ta Kano, Farm Center da rana tsaka.
Sun fasa wasu gilasan da ake ajiye wayoyin inda hakan ya kawo tarnaki sosai.
Rahoton yace tsageran sun ci zarafin mutane inda suka kwace wayoyi.
Daga baya dai an samu nutsuwa inda jami’an tsaro suka kai samame wajan.

