Friday, June 26
Shadow

Bidiyon shahararren me sayar da mota, Manga Automobiles ya bayyana yana soyayya da wata mata, Saidai yayi karin bayani inda yake an dauki Bidiyon ne da dadewa tun kamin yayi aure lokacin suna soyayya da wadda aka ganshi a Bidiyon

Bidiyon shahararren me sayar da motoci, Manga Automobiles ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ganshi yana soyayya da wata Budurwa.

Da yawa dai sun yi mamakin ganin Bidiyon musamman ganin cewa ana masa kallon Mutum me kamala wanda da yawa ke ganin girmansa.

Saidai a nasa martanin ya tabbatar da cewa shine a Bidiyon amma tsohon Bidiyo ne wanda aka dauka tun kamin yayi aure lokacin yana soyayya da wadda aka gansu tare a Bidiyon.

Yace bai ji dadin watsa Bidiyon ba kuma zai dauku matakin shari’a kan wadanda suka watsa Bidiyon.

Karanta Wannan  A karshe dai Sojoji sun kubutar da matar Marigayi Janar Rabe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *