Wednesday, February 25
Shadow

Hukumar ‘yansandan kasar Ghana ta gargadi matan aure cewa duk matar data hana mijinta mu’amalar aure, Zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari

Jami’in Hukumar ‘yansandan kasar Ghana, (ACP), Dennis Fiakpui yace takura a aure da saka damuwa babban laifine a kasar.

Yace a tsakanin ma’aurata, duk wanda ya hana dan uwansa ma’amalar aure, misali mace ta ki yadda da mijinta a gado, idan ya kai kara kuma kotu ta samu matar da laifi, zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari.

Yace hakanan itama idan macence mijinta baya kwanciyar aure da ita, zata iya kaishi kara a nema mata hakkinta.

Yace hakanan idan miji na dadewa a waje baya komawa gida da wuri ko kuma ya daina cin abincin matarsa, duka zata iya kaishi kara a bi mata hakkinta.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan yaronnan dan shekaru 18 da ya dirkawa 'yan mata 10 ciki tare da 'yan matan da yawa ciki su 10

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *