
Hukumar ‘yansandan Najeriya na shirin kammala jarabawar daukar sabbin ‘yansandan da aka fara a tsakanin shekarun 2022/2023.
Me magana da yawun hukumar ta PSC,Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manem labarai.
Yace abu na gaba da za’a yi yanzu shine gwajin lafiyar wadanda za’a dauka aikin wanda zai fara daga February 26 zuwa March 12, 2025.
Ya kara da cewa, wadanda suka yi jarabawar kwamfuta a ranekun 5th zuwa 6th March, 2024 amma sunayen su basu fito cikin wadanda suka yi nasara ba su sake zuwa shafin daukar aikin su duba ko sunayensu sun fito.
Yace za’a yi gwajin lafiyar sabbin daukar aikinne a Asibitoci 17
Yace za’a bude shafinne a ranar February 22nd, 2025 da misalin karfe 12 na rana.
Yace kuma duk wadanda aka gayyata zuwa wajan gwajin lafiyar su tabbatar sun je da fararen riga me gajeren hannu da gajeren wando.
Sannan yace kowa ya tabbatar ya je a daidai lokacin da aka rubuta a jikin takardar gayyatar tasa.