Friday, December 26
Shadow

Idan zaka iya ko kasan wani wanda zai iya, ana neman wanda zai iya yin zaman gidan Yarin Kuje dake Abuja na tsawon watanni 6, za’a rika biyan Naita Miliyan 1 duk wata

Wata sanarawa ta bayyana a kafafen sada zumunta inda ake neman wanda zai iya yin zaman gidan yarin Kuje dake Abuja na tsawon watanni 6.

Za’a rika biyan Naira Miliyan 1 duk wata, zai bayar da sunan wani na kusa dashi ne da za’a rika baiwa kudin.

Sannan idan ya fito za’a bashi Naira Miliyan 5 dan ya kula da lafiyarsa.

Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki.

Saidai a shekarun baya, Hutudole ya taba ruwaito muku cewa, babban lauya, Femi Falana ya bayar da labarin cewa irin haka na faruwa.

Karanta Wannan  Rikicin kabilanci ya janyo mùtùwàr mutum tara a Jigawa

Idan aka yankewa wani shahararre hukunci, tun kamin aje gidan yarin akan hanya ko kumama a cikin kotun za’a rika tattaunawa a samo wanda zai yi zaman gidan yarin a biyashi, shi kuma wanda akawa hukuncin ya tafi gida.

1 Comment

Leave a Reply to Aliyu Faruq Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *