‘Yar Fim din kudancin Najeriya, Yvonne Jegede ta bayyana cewa, irin namijin da take so shine wanda idan ta tambayeshi kudi, zai bata fiye da abinda ta tambaya ba tare da ya tambayeta me zata yi dasu ba.
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita.
Tace tana son mijin da idan ta tambayeshi Miliyan 1, zai bata miliyan 20.
Ba wanda idan ta tambayeshi ba zai zageta yace mata kudin ubanta ne?