Jami’in hukumar tsaro ta NSCDC Opatola wanda ba’a dade da karawa mukami ba ya yanke jiki ya fadi ya mutu jim kadan bayan an biyashi Albashi.
Yana aiki ne a Iwo kuma ya mutu ne bayan da ya shiga ban daki kamar zai biya bukatarsa.
Wasu shaidu sun bayyanawa jaridar The Nation cewa mutumin ya je wajan aiki lafiya kalau a ranar da ya mutu.
Abokan aikinsa sun ce sun ga Albashinsu suna korafi akai jim kadan kawai aka ce ai ya mutu.