Matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Hadiza El-Rufai ta yiwa sanata Sanata Shehu Sani gyaran kuskuren Turancin da yayi a shafinsa na Twitter.
Saidai da alama Sanata Sani bai ji dadin wannan gyara da ta masa ba inda mata martani da cewa, mun daina bibiyar juna a kafafen sada zumunta dan Allah ki kyaleni.
Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda wasu ke cewa ya kamata ya karbi gyaran da aka masa wasu kuma na goyon bayanshi.