
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ba kudi Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi ya masa yakin neman zabe ba.
Yace shi tunda yasan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai taba bashi ko sisi ba ko da kudin siyen Pure Water.
Yace amma ba zai iya rantsuwa akan sauran wadanda sukawa Tinubu yakin neman zabe ba amma shi dai ba’a bashi ko sisi ba.