
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi da tsohon Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi sun hadu a fadar Vatican wajan rantsar da sabon Fafaroma Leo XIV.
Kayode Fayemi ne yawa Peter Obi jagoranci zuwa wajan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda ya fara magana da cewa, Shugaban kasa barka da zuwa cocin mu, mun gode da ka amsa gayyatar Fafaroma.
Tinubu ya amsa da cewa nine ya kamata ace na muku barka da zuwa.
Yace nine shugaban tawagar Najeriya a wannan taron, sun amsa masa da cewa dukkansu suna karkashin Tawagarsa.